Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jaridar Al-Nahar ta kasar Labanon ta bayar da rahoton cewa, Masar na cikin shirin ko ta kwana domin tunkarar wani shiri na yahudawan sahyuniya na kwashe al'ummar Palastinu daga kudancin zirin Gaza zuwa cikin hamadar Sinai.
A cewar jaridar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta sanar da isar kayayyakin aiki da tantuna a zirin Gaza a ranar Lahadin da ta gabata, domin tilastawa al'ummar birnin Gaza yin hijira zuwa kudu kusa da kan iyaka da Masar.
Wannan mataki dai ya haifar da tuhuma da nuna damuwa game da sabon yunkurin da majalisar ministocin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila karkashin jagorancin "Benjamin Netanyahu" ke yi na mayar da 'yan kasar Falasdinawa zuwa yankunan da ke wajen zirin Gaza ciki har da yankin Sina'i na kasar Masar, a wani bangare na shirin kawar da batun Palasdinawa da kuma yunkurin kafa kasar Falasdinun.
Your Comment